Home Labaru Ina Atiku Ya Je A Ranar Rantsuwa?

Ina Atiku Ya Je A Ranar Rantsuwa?

251
0

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar,
ya halarci bikin rantsar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a
matsayin gwamnan jihar Adamawa a wa’adi na biyu.

An dai rantsar da Fintiri domin jagorancin jihar Adamawa wadda ita ce mahaifar Atiku, karo na biyu bayan ya yi nasara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Atiku ABubakar, ya ce ya bi sawun al’ummar Jihar Adamawa wajen taya Gwamna Fintiri da mataimakiyar sa Farfesa Kaletapwa Farauta murnar nasara da kuma rantsuwar kama aiki a karo na biyu.

A ranar Talatar nan ne kotun sauraren ƙararrakin zaɓe za ta cigaba da zaman sauraren shari’ar da ke ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu, wadda Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP su ka shigar duk da cewa an rantsar da shi.

Leave a Reply