Home Labaru Gwamnatocin Baya Su Yi Bayani Kan Kuɗaɗen Abacha Da Aka Ƙwato –...

Gwamnatocin Baya Su Yi Bayani Kan Kuɗaɗen Abacha Da Aka Ƙwato – Kotu

318
0

Wata Babbar Kotun Tarayya ta bada umarnin cewa, a bayyana
yadda aka kashe kuɗaɗen da yawan su ya kai Dala biliyan
biyar da ake zargin tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha
ya sace amma aka maido wa Nijeriya.

Bayanai sun ce, an maido wa Najeriya kuɗin da ake kira da ‘satar Abacha’ a lokacin mulkin shugabannin Nijeriya, kamar Olusegun Obasanjo da Umar Musa Yar’adua da Goodluck Jonathan da kuma Muhammadu Buhari.

Kotun, ta kuma umarci gwamnatin shugaba Tinubu ta bayyana takamaiman yawan kuɗin da marigayi Sani Abacha ya sace, da kuma duk abin da aka gano tun bayan dawowar Nijeriya mulkin dimokraɗiyya.

Kungiyar Transparency International mai fafutukar yaƙi da rashawa ta ƙiyasta cewa, marigayi Abacha ya wawure dukiyar Najeriya da ta kai dala biliyan biyar, inda ta ce kuma babu wanda ya taɓa gurfanar da shi gaban kotu a kan lamarin.

Kungiya mai rajin yaƙi da hanci da rashawa a Nijeriya SERAP ce ta shigar da ƙara gaban kotun, inda ta buƙaci a tilasta wa gwamnati ta bayyana kuɗaɗen almundahanar Abacha.

Leave a Reply