Real Madrid ta fara kare kofin La Liga da tashi 1-1 a gidan Real Mallorca ranar Lahadi a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Real ta fara cin ƙwalllo ne ta hannun Rodrygo a minti na 14 da take leda, haka suka je hutu, Real tana da ƙwallo ɗaya a raga.
Bayan da suka je hutu suka koma zagaye na biyu ne mai masukin baƙi ta farke ta hannun Vedat Muriqi.
Real ta kare wasan da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ferland Mendy jan kati daf da za a tashi, sakamkon ketar da ya yi wa Vedat Muriqi.
A kakar bara a gasar ta La Liga, Real doke Mallorca 1-0 ta yi gida da waje.
Ranar Asabar, Barcelona ta je ta ci Valencia 2-1 a wasan makon farko a La Liga.
Ranar Laraba Real Madrid mai rike da La Liga na bara ta ɗauki Uefa Super Cup na bana, bayan da ta ci Atalanta 2-0 a Warsaw a Poland.
Real ce ta lashe kofin La Liga a kakar da ta wuce da kuma Champions League.
Za a kammala wasannin makon farko a La Liga ranar Litinin 19 ga watan Agusta, inda za a kara tsakanin Valladolid da Espanyol da na Villarreal da Atl Madrid.