Home Labaru Ba Zan Janye Wa Kowa Ba, Amma Na ‘Jone’ Da Guruf Ɗin...

Ba Zan Janye Wa Kowa Ba, Amma Na ‘Jone’ Da Guruf Ɗin Abdul’Aziz Yari – Orji Kalu

444
0

Mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa Sanata Orji Kalu, ya ce
bai janye wa kowa ba kuma ba zai janye kudirin sa na neman
kujerar shugaban majalsar ba.

Sanata Orji Kalu, ya ce har yanzu ya na nan a kan bakan sa na takarar shugaban majalisar dattawa, domin shugabancin majalisa kamar shugabancin Nijeriya ne, babu wani yanki da zai iya kawo shugaban ƙasa ko shugaban majalisar dattawa shi kadai.

Ya ce yanzu haka masu goyon bayan sa sun haɗe da masu goyon bayan Sanata Abdul’aziz Yari domin su samu matsaya ɗaya a tsakanin su.

A wani bangare kuma, sanatocin jam’iyyar APC na yankin Arewa ta Tsakiya, sun ce Sanata Sani Musa daga Jihar Neja su ke so ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, yayin da Sanata Osita Izunaso daga jihar Imo ya nemi a saka masa wahalar da ya yi wa jam’iyyar APC da mukamin shugabancin Majalisar Dattawa.

LEAVE A REPLY