Hukumar Zaɓe mai zaman kan ta ta Ƙasa INEC, ta ce bijiro da wasu ƙwararan matakai huɗu da ta yi sun tabbatar da cewa babu wata hanya da za a iya bi a yi maguɗin zaɓen shekara ta 2023.
Matakin farko shi ne, dabarar tantance wanda ya yi rajistar mallakar katin zaɓe sau biyu ko fiye da haka, da amfani da na’urar tantance adadin masu zaɓe a rumfunan zaɓe, tsarin da ya ke maganin masu satar ƙuri’u ko ɓarayin akwatin zaɓe.
Sai mataki na uku kuma shi ne manhajar tattara sakamakon zaɓen da kowa zai iya gani ido-da-ido.
Da ya ke jawabi a wajen taron zaburar da matasa muhimmancin zaɓe a Enugu, Mataimakin Sakataren hukumar zaben Injiniya Chidi Nwafor, ya ce Dokar Zaɓe ta shekara ta 2022 ita ce matakin hana maguɗin zaɓe na huɗu.














































