Home Labaru Hana Sa Hijabi: Iyayen Dalibai Sun Gargadi Shugabar Makarantar Sakandare Ta Isi

Hana Sa Hijabi: Iyayen Dalibai Sun Gargadi Shugabar Makarantar Sakandare Ta Isi

274
0

Ana ci-gaba fafatawa tsakanin iyaye da hukumar makarantar sakandare ta jami’ar Ibadan game da batun hana dalibai mata sanya hijabi.

Yanzu haka dai iyayen dalibai sun zargi shugabar makarantar Misis Phebean Olowe da laifin rura wutar wani rikici a makarantar, ta hanyar kuntata wa dalibai mata Musulmi masu neman a bar su su na sanya hijabi a cikin makaranta.

Kungiyar Iyayen Dalibai Musulmi na makarantar ta yi wannan zargi a birnin Ibadan na Jihar Oyo, inda yayen daliban su ka yi ikirarin cewa hukumar makarantar ta na muzguna wa dalibai mata Musulmi masu zuwa makarantar sanye da hijabi.

Idan dai ba a manta ba, tun cikin watan Nuwamba na shekara ta 2018 ne, batun sanya hijabi ya zama rikici a makarantar, har ta kai ga kungiyar iyayen dalibai suka maka makarantar, da Jami’ar Ibadan da kuma Hukumar Gudanarwa ta makarantar kotu.

Sai dai a ranar 26 Ga Yuni, wata Babbar Kotun Jihar Oyo ta kori karar, bisa dalilin cewa wadanda su ka shigar da karar ba su da hurumin kai kara a kungiyance.

Leave a Reply