Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya nesanta kan sa da wasu kalaman da ya ce ba daidai ba ne, kuma masu hatsari da wasu ke alaƙantawa da shi.
Wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran sa ya fitar, ta ruwaito Kashim Shettima ya na cewa kalaman da aka ce ya furta wasu ‘yan jamhuru ne su ka kitsa su, a yunƙurin su na nuna rashin dacewar ‘yan takara Musulmai da ke neman shugabancin Majalisar dattawa.
Sanarwar dai ta zo ne, bayan a wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, an ambato Kashim Shettima ya na cewa, a wajen sa idan ana maganar wannan gwamnatin, Kirista mafi lalacewa kuma mafi rashin ƙwarewa daga Kudu ya fi Musulmin Arewa na-ƙwarai cancantar zama shugaban majalisar dattawa.
Ya ce ba a bayyana kalaman a muhallin da aka yi su ba, kuma an canza masu ma’ana don kawai su dace da manufar masu zagon ƙasa ga burin al’ummar Nijeriya na tabbatar da haɗin kan ƙasa.
Sanarwar ta cigaba da cewa, Kashim Shettima ya jaddada tsarin siyasar Nijeriya ne kawai, inda ya yi nuni da cewa samun Kirista daga kudancin Nijeriya da wani Musulmi daga Arewa shi ne zai tabbatar da daidaiton adalci domin inganta muradin shigar da kowa a dama da shi.

