Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ina Neman Afuwar Musulmai Kan Kalamaina – Kashim Shettima

Maitamakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima, ya ce ya
na neman afuwar al’ummar Musulmi bisa wasu kalamai da ya
yi game da zaɓen shugabannin majalisar dokoki ta tarayya.

Kashim Shettimsa ya ce ba a fahimci maganar a muhallin ta ba, kuma ba ya da wata manufa ta ɓata sunan addinin sa.

Ya ce ya furta kalaman ne saboda maslahar Nijeriya, ganin cewa su na da wasu bayanan sirri da bai dace ya fito bainar jama’a ya na bayani a kan su ba.

Kalaman Kashim Shettima dai sun haifar da zazzafar muhawara musamman a shafukan sada zumunta, sai dai ya ce shi Musulmi ne na haƙiƙa, domin zuri’ar su sun shafe tsawon shekaru a kan tafarkin addinin.

A karshe ya ce duk wanda bai ji dadin kalaman sa ba ya yi hakuri a yafe ma shi, domin ba ya da niyyar cutar da addinin Musulunci.

Exit mobile version