Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tabbatar Da Takara: Tinubu Zai Gabatar Da Kashim Shettima A Matsayin Mataimakinsa

Dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, zai gabatar da tsohon gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ga ‘yan kasa a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.


Wata sanarwa da jam’iyyar APC ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Talata nan ta ce za a gabatar da Sanata Shettima ne ranar laraba, 20 ga watan Yulin 2022.


Za a yi bikin gabatar da shi ne a babban dakin taro na Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja da misalin karfe 11 na safe.


A makon jiya ne Bola Tinubu ya sanar da zaben tsohon Gwamnan Jihar Borno kuma Sanata mai wakiltar tsakiyar Borno, Kashim Shettima, a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaben 2023.


Sai dai batun ya jawo muhawara mai zafi inda wasu ke ganin bai dace Tinubu, wanda Musulmi ne daga kudancin Najeriya, ya zabi Shettima, wanda Musulmi ne daga Arewacin kasar nan a matsayin mataimakinsa ba.


Amma jam’iyyar APC da ma Tinubu sun ce zabensa ba shi da alaka da addini.

Exit mobile version