Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kashim Shettima Ya Ce Sanata Akpabio Ya Cancanci Jagorantar Majalisar Dattawa

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya ce Sanata
Godswill Akpabio ne ya cancanci zama shugaban majalisar
dattawa.

Kashim Shettima ya bayyana haka ne, a wajen wata liyafa da ‘yan tawagar yaƙin neman zaɓen Akpabio su ka shirya a masaukin baki na Transcorp Hilton da ke Abuja.

Shettima ya kara da cewa, Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC su na goyon bayan Godswill Akpabio ne saboda ya fito daga yanki mai muhimmanci a Nijeriya.

Ya ce sun cimma matsayar ne domin ta yi daidai da yawan haɗin kan da ake buƙata a Nijeriya.

Exit mobile version