Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zaben 2023 Ne Mafi Inganci A Tarihin Nijeriya –Gbajabiamila

Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ya ce zaben shekara ta 2023 ya kasance mafi inganci da aka taba gudanarwa a tarihin Nijeriya.

Femi Gbajabiamila, ya ce an samu ci-gaba a kokarin Nijeriya  na tabbatar da sahihin zabe.

Wannan dai ya na zuwa ne, a daidai lokacin da Gbajabiamila ya tabbatar da cewa, majalisar za ta tabbatar da amincewa da kudirin dokar hukumar laifuffukan zabe kafin karewar wa’adin ta a watan Yuni.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne a Abuja, yayin da ya ke maraba da takwarorin sa, wadanda su ka dawo daga zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da aka kammala, inda ya ce sun tabbatar an samu ci-gaban da aka samu a kokarin da su ke yi na tabbatar da zaben da za su yi alfahari da shi. Ya ce gyaran dokar zabe da majalisar dokoki ta tarayya ta yi, ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin zabe ta hanyar amfani da na’urorin fasaha domin saukaka tantance masu kada kuri’a da yada sakamakon zabe.

Exit mobile version