Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Nasarar APC: PDP Ta Taya Sabbin Shugabanni Masalisun Tarayya Murnar Lashe Zabe

Jam’iyyar PDP ta taya sabon shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan da sabon kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila murnar lashe zabe da su ka yi.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Talatar da ta gabata ne aka rantsar da Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamilla a matsayin shugabannin majalisun dokoki na tarayya bayan kammla zabe a zauran majalisun.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa dole ne majalisa ta tara ta yi kokari wajen ceto Nijeriya daga halin ha’ula’in da gwamnatin shugaba Buhari ta jefa ta ciki, musamman samar da ingantaccen shugabanci da kowa karshen satar dukiyar al’umma.

A karshe jam’iyyar PDP ta ce ta na nan a kan akidar ta na kare ‘yancin damukaradiyya, kuma ta na sa ran dan takarar ta azaben 2019 Atiku Abubakar zai kwace nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben ta hanyar karba a kotu.

Exit mobile version