Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Taya Murna: Bukola Saraki Ya Yi Wa Lawan Da Gbajabiamila Nasiha

Tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya taya sabon zababben shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, da mataimakainsa, Sanata Ovie Omo-Agege, da kuma sabon zababben shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da mataimakinsa, Idris Wase, murnar lashe zabe.
A sakon da ya fitar a shafinsa da Tuwita, Saraki, ya shaidawa sabbin shugabannin cewar sune zasu jagoranci majalisa karo na 9 na tsawon zango guda (shekara hudu).
A gana wa ta karshe tsakanin bangaren zartar wa da shugabancin majalisa da aka yi cikin azumi a fadar shugaban kasa, shugaba Buhari ya ce bai ji dadin mulki da majalisar da Saraki da Dogara suka jagoranta ba.
A wata hira da aka yi da shi kai tsaye a gidan Talabijin na kasa (NTA), wacce sauran kafafen yada labarai suka watsa, Buhari ya ce ba zai saka Saraki da Dogara da majlisar tarayya karo na 8 a cikin ‘yan kishin kasa ba.
Sanata Ahmed Lawan, danlelen shugaban kasa da jam’iyyar APC a zaben shugaban majalisar dattijai, ya samu nasarar buga abokin hamayyarsa da jam’iyyar PDP ke mara wa baya, sanata Ali Ndume, da kasa a zaben da aka yi yau, Talata.
Lawan ya zama sabon shugaban majalisar dattijai bayan ya samu adadin kuri’u 79, yayin da abokin takararsa kuma shalelen jam’iyyar PDP, Sanata Ndume, ya samu kuri’u 28 kacal.

Exit mobile version