Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yadda Rundunar Yan Sanda Ta Shirya Wa Zaben Cike Gurbi Na Gobe Asabar

Gabanin zaben cike gurbi da za a yi ranar Asabar din nan,
shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya ya ba masu kada
kuri’a tabbacin kare lafiyar su a rumfunan zabe.

Usman Alkali Baba, ya kuma bada umarnin tura ‘yan sanda zuwa kananan hukumomi 185 a fadin jihohi 24 na tarayyar Nijeriya, inda za a sake gudanar da zaben.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce Alkali Baba ya bada umarnin tura isassun jami’ai da ke tallafawa da kuma Karin kayan aiki domin samar da ingantaccen tsaro a zaben da za’a gudanar a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu.

Sanarwa ta kara da cewa, karin tallafin ya hada da tura ma’aikata da motocin aiki da makamai da rigunan kare kai da kayan yaki da tarzoma da dai sauran su.

Shugaban ‘yan sandan, ya kuma umarci manyan jami’an ‘yan sanda da ke kula da wasu yankunan da za a gudanar da zaben, musamman zaben gwamnoni a jihohin Adamawa da Kebbi, su tabbatar da samar da isasssun ma’aikata da sauran kayan aiki domin gudanar da ingantaccen aikin ‘yan sanda.

Exit mobile version