Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sojoji Sun Kama Kwamandan ISWAP A Neja Sun Kashe ‘Ƴan Bindiga A Kaduna

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe ƴan bindiga bakwai a Jihar Kaduna tare da ƙwato makamai.


Haka kuma wasu rahotannin na cewa sojojin sun daƙile wani hari da aka kai musu a wani sansanin su da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja inda suka kama kwamandan ƙungiyar ISWAP.


A wani saƙo da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebbok, ta bayyana cewa tun da farko dakarun Operation Safe Forest Sanity ne suka ƙaddamar da wani samame a Maidaro da Tudun Kagi da Kusharki da kuma Anguwan Madaki duka jihar.


A yayin samamen, sojojin sun yi musayar wuta da ƴan bindigar inda suka kashe ƴan bindigar huɗu tare da ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da harsasai samfarin 7.62mm da kuma bindiga ƙirar Pump Action ɗaya da harsasai uku da ƙananan bindigogi da babura huɗu.


A wani samame a yankunan Sabon Birni-Zartake da Ungwan Lima Riyawa da Tungan Madaki sojojin sama sun yiwa ƴan bindigar da ke tserewa daga Tudun Kagi kofara rago, tareda kashe uku daga cikin su.

Exit mobile version