Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji Biyar A Kaduna

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce dakarun ta sun kashe ‘yan bindiga biyar tare da ƙwato makamai a wani samame da ta kai dajin Kubusu da tsaunukan Kaso a yankin Chikun na jihar Kaduna.

Wata sanarwa da mai riƙon muƙamin jami’in hulda da jama’a na runduna ta 1 da ke Kaduna, Laftanal Kanar Musa Yahaya ya fitar, ta ce dakarun sojin sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK 47 shida, da harsasan bindigogi da wasu ƙarin albarusai, da babura uku da ƙarin wasu kayayyaki.

Ya ce a lokacin artabu da ‘yan ‘yan bindigar, dakarun sojin sun samu nasarar fatattakar gungun mahara tare da kashe biyar daga cikin su, sannan su ka ƙwato makamai masu tarin yawa.

A ƙarshe sanarawar ta ambato babban kwamandan runduna ta 1 da ke Kaduna Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya na yaba wa dakarun sojin bisa wannan namijin ƙoƙari da ya ce sun yi a lokacin fafatawar.

Exit mobile version