Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ribadu: Mun Kama ’Yan Siyasar Da Suka Ba Masu Zanga-Zanga Kudi

National Securuty Adviser Nuhu Ribadu e1716792973301

National Securuty Adviser Nuhu Ribadu e1716792973301

Nuhu Ribadu, ya sanar da kama wasu ’yan siyasa da suka ba da gudunmawar Naira biliyan hudu domin gudanar da zanga-zangar kyamar yunwa a Najeriya.

Nuhu Ribadu ya ce an kama ’yan siyasan ne a babban birnin tarayya Abuja da jihar Kano, da Kaduna da kuma Katsina kan laifin kasancewa daga cikin masu daukar nauyin masu zanga-zangar.

Ya sanar da hakan ne dai a yayin gabatar da rahoto ga taron Majalisar Kasa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a nan Abuja.

Taron na ranar Talata ya samu halartar tsaffin shugabannin kasa irin su Muhammadu Buhari, da Goodluck Jonathan, da Abdulsalam Abubakar da kuma Yakubu Gowon.

Jonathan da Buhari sun bayyana goyon baya da kwarin gwiwa cewa gwamantin Tinubu za ta jagoranci Najeriya zuwa tudun mun tsira.

Taron shi ne na farko na farko da Tinubu ya kira tun bayan hawan sa mulki a ranar 29 ga watan Mayu,

2023, kuma ya tattauna kan zanga-zangar da aka gudanar da matsalolin yunwa, da tsaro da na tattalin arziki ne.

Exit mobile version