Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rikicin Shi’a: An Kashe ‘Dan Sanda Da Mai Yi Wa Kasa Hidima

An tabbatar da mutuwar mataimakin kwamishinan ‘Yan sandan Najeriya, Usman Umar da wata matashiya mai yiwa kasa hidima, Precious Owolabi, sakamakon raunin bindigar da suka samu a sabuwar tarzomar mabiya akidar Shi’a da ta barke a Abuja.

mataimakin kwamishinan ‘Yan sandan Najeriya, Usman Umar

Rahotanni sun ce, masu zanga-zangar ne suka harbe mataimakin kwamishinan ‘Yan sandan, a yayinda ya rasu a daidai lokacin da yake karbar magani a asibiti.

Ita kuwa Owolabi mai shekaru 23 dake yi wa hidimar kasa a gidan talabijin na Channels, a cikin daren da ya gabata ne aka tabbatar da mutuwarta, bayan harsashin bindiga ya same ta a daidai lokacin da take bakin aikin daukar rahoton arangamar tsakanin ‘yan sanda da ‘yan Shi’a.

A bangare guda mai magana da yawun kungiyar ‘yan Shi’a a Najeriya, Ibrahim Musa ya ce, an kashe musu mabiya akalla 11, yayinda aka raunata da dama daga cikin su.

Mabiyan Shi’ar dai sun gudanar da zanga-zangar ce da zummar matsin lamba kan gwamnati domin ganin ta saki jagoran su, Ibrahim Zakzaky da ke tsare.

Tuni jamai’an tsaro suka kama mutane da dama da ake zargin alakarsu da masu zanga-zangar.

Exit mobile version