Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zanga-Zangar IPOB: Mutum Biyu Sun Mutu A Enugu

Rahotanni daga Jihar Enugu na cewa mutum biyu sun mutu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin ‘yan ƙungiyar IPOB masu son ɓallewa daga Najeriya da kuma jami’an ‘yan sanda.

Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi kuma an jikkata wasu dama daga cikin ‘ya’yan ƙungiyar da suka fito zanga-zangar.

Kazalika, jaridar The Nation ta ce an kama wasu da yawa daga cikinsu, sai dai wani da ya shaida lamarin ya faɗa wa jaridar Punch cewa mutum 10 aka kama.

Exit mobile version