Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Mazauna Yankunan Jihar Katsina Na Fargaba Saboda Kwararar ‘Yan Bindiga

Tabbatattun bayanai sun nuna cewa, ɗaruruwan ‘yan bindiga a ƙarƙashin fitinannen ɗan ta’addan nan mai laƙabin Ɗanƙarami  sun yi hijira daga Zamfara, sun kwarara zuwa ƙananan hukumomin Safana da Batsari a Jihar Katsina.

Mazauna ƙauyukan da su ka riƙa ganin kwararar maharani, sun ce ‘yan bindigar sun yi hijira daga jihar Zamfara ne saboda fatattakar su da sojoji ke yi a halin yanzu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, an ga irin su a yankunan Tsaskiya da Runka da Gora II da Labo da wasu ƙauyukan ƙananan Hukumomin biyu.

Mazauna yankin sun ce, gudaddun ‘yan bindigar sun haɗe da gungun dabar ɗan ta’adda Usman Moɗi-Moɗi, wanda yanzu haka ke yawan kai wa mutane hari.

Exit mobile version