Tabbatattun bayanai sun nuna cewa, ɗaruruwan ‘yan bindiga a
ƙarƙashin fitinannen ɗan ta’addan nan mai laƙabin Ɗanƙarami
sun yi hijira daga Zamfara, sun kwarara zuwa ƙananan
hukumomin Safana da Batsari a Jihar Katsina.
Mazauna ƙauyukan da su ka riƙa ganin kwararar maharani, sun ce ‘yan bindigar sun yi hijira daga jihar Zamfara ne saboda fatattakar su da sojoji ke yi a halin yanzu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, an ga irin su a yankunan Tsaskiya da Runka da Gora II da Labo da wasu ƙauyukan ƙananan Hukumomin biyu.
Mazauna yankin sun ce, gudaddun ‘yan bindigar sun haɗe da gungun dabar ɗan ta’adda Usman Moɗi-Moɗi, wanda yanzu haka ke yawan kai wa mutane hari.
Tuni dai Mazauna yankunan sun roƙi jami’an Soji da Gwamnatin Jihar Katsina su ɗauki matakan gaugawa, domin hana ‘yan ta’addan fara kai wa al’ummar yankunan hare-hare.

