Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Bindiga 300 Sun Kai Hari A Kauyukan Katsina

'Yan Bindiga

'Yan Bindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Katsina ta ce wasu ‘yan bindiga 300 sun far wa kauyukan Kirtawa da Kinfau da Zamfarawan Madogara da ke yankunan kananan hukumomin Batsari da Safana

Karanta Wannan: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 A Katsina

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Gambo Isah ya fitar, ya ce hare-haren da aka kai a ranar Asabar sun yi sandiyyar mutuwar mutune 10 tare da jikkata wasu biyar.

Gambo Isah ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun rika harbin kan mai uwa da wabi inda suka tarwatsa mutanen kauyen, sannan suka cinna wa ababan hawan mutane wutan, bayan sun kora shanun da ba a san adadin su ba.

Wani wanda harin ya rutsa da shi a kauyen Zamfarawan Madogara ya bayyana yadda lamarin ya auku, inda ya ce ‘yan bindigar su na sace mata a duk lokacin da suka kai hare-hare kauyukan su.

Exit mobile version