Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Majalisar Kaduna Ta Ce El-Rufai Ya Yi Riga Mallam Masallaci

el rufai (2)

el rufai (2)

Majalisar dokokin ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar El-Rufai ya shigar gaban wata kotun tarayya inda yake kalubalantar rahoton

Majalisar da ya zarge shi da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin mulkin sa.

Shi dai tsohon gwamnan na zargin Majalisar ne da take masa hakki kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanadar.

Majalisar dokokin jihar Kaduna a martanin da ta mayar, ta ce ta yi matukar mamaki ne kan yadda tsohon gwamnan ya ruga zuwa kotu,

yana kalubalantar sakamakon binciken da kwamitinta ya gudanar, tana mai cewa yin hakan tamkar riga Malam Masallaci ne.

Mai magana da yawun Majalisar dokokin jihar Kaduna, ya ce an mika rahoton ne domin a ci gaba da bincike kuma za a kira shi.

Exit mobile version