Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsige El-Rufai: Shugaban Majalisar Kaduna Ya Karyata Raderadin Da Ake Yadawa

Shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Zailani ya karyata raderadin da ake ta yadawa wai majalisar za ta tsige gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.


Yusuf Zailani ya karyata labarin ne a wata sanarwa da ofishin sa ta fitar ranar Lahadi, yana mai cewa makiyan jihar Kaduna ne suka kitsa wannan makirci domin raba kan majalisar da kuma tarwatsa zaman lafiya dake tsakanin majalisar da gwamna Nasir El-Rufai.


An dai buga a wasu shafukan ƴaɗa labarai ne cewa majalisar dokin jihar Kaduna ta gano wasu harkallar makudan kudade da aka yi sama da fadi da su a wasu ma’aikatun gwamnatin jihar wanda da sanin gwamnan aka handame su, inda ta fadada bincike kuma ta gano cewa lallai an aikata hakan wannan shi ne dalilin da ya sa za ta tsige gwamnan jihar.


Sai dai shugaban majalisar dokokin jihar Kadunan yace babu magana mai kama da wannan, wasu ne kawai da basu son suga ana zaman lafiya suka kitsa haka, amma tsakanin majalisar jihar Kaduna da bangaren zartarwa, suna zaman lafiya babu wani abu da ya shiga tsakanin su.


Yusuf Zilani, ya yi kira ga mutanen jihar Kaduna su yi watsi da wannan labari su cigaba da al’amuran su, akwai aminci da kauna a tsanin gwamna El-Rufai da majalisar jihar.

Exit mobile version