Dan majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu da ta
Gabas a Majalisar Wakil Dachung Musa Bagos, ya yi kira ga
jama’ar yankin sa su tashi su kare kan su daga kashe-kashe da
haren-haren da ake kai masu.
Musa Bagos, ya nuna baƙin cikin sa a kan sabbin hare-haren da aka kai a yankunan Mangu da Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a ranakun Asabar da Lahadin da su ka gabata, inda aka kashe sama da mutane 20.
Dan Malajisar, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya musamman mazauna ƙauyukan Filato da lamarin ya shafa, su miƙe su kare kan su daga hare-haren da su ke fuskanta.
Ya ce abin baƙin cikin shi ne, ana kai hare-hare da kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba kowace rana a Jihar Filato, musamman a yankunan Riyom da Barkin Ladi da Mangu.

