Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kin Jinin Baki: Geoffrey Onyeama Ya Ce Hakurin Nijeriya Ya Kare

Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya

Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya, ta ce hakurin ta ya kare a kan hare-haren da ‘yan Afirka ta kudu ke kai wa ‘yan kasar ta da ke zama a can.

Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya bayyana haka, a cikin sakon da ya aike ta shafin sa na twitter, inda ya ce Nijeriya ba za ta lamunci yadda wasu bata-gari ke kai hari a kan mutanen ta ba.

Wannan mataki dai ya biyo bayan harin da aka kai wa ‘yan Nijeriya a karshen makon da ya gabata, inda aka kashe mutane uku, tare da kona shagunan su a unguwar Jeppestown da ke birnin Johannesburg.

Lokuta da dama dai, Cyril Ramaphosa na kasar Afrika ta Kudu, ya na nuna damuwa da kisan ‘yan Nijeriya a kasar sa, musamman yayin ganawar sa da shugaba Buhari da kuma manema labarai.

Shugaban ‘ynan Nijeriya mazauna kasar Afirka ta kudu Adetola Olubajo, ya ce akwai wata kungiyar bata-gari da ake kira ‘Zulu Dwellers’, ita ke da alhakin kai hare-hare a kan shaguna da wuraren sana’ar baki musamman ‘yan Nijeriya.

Exit mobile version