Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce wasu daga
cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta sun samo asali ne tun
daga lokacin turawan mulkin mallaka.
Obasanjo, ya bayyana haka ne yayin gabatar da wata maƙalar littafi a ranar Asabar a Enugu,inda ya kara da cewa duk tsarin da aka gabatar na tattalin arziki matukar babu gwamnatin mai manufa ga kuma gurgun tsari da ake fama da shi, wadannan abubuwan sai sun durkusar da tsarin.
Tsohon shugaban ya ce akwai alaka tsakanin tattalin arziki da sauya tsarin siyasa a Najeriya, inda ya kara da cewa tarihin yadda aka samar da kundin tsarin mulkin Najeriya da tubalin da aka dora siyasar kasar sun nuna akwai wani gurbi da aka bari, wanda yake bukatar a cike shi.
Kazalika, ya ce matuka ba’a samu jajirtattun shugabanni da za su tabbatar da tsarin da ya dace da kuma cike gibin matsalolin da Najeriya ta gada tun turawan mulkin mallaka, abu ne mai wuya a samu sauyin da ake muradi.

