Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Obasanjo Ya Sake Rubuta Wa Shugaba Buhari Wasika

Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa

Olusegun Obasanjo, Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya sake aike wa shugaba Muhammadu Buhari wasika, inda ya ke gargadin shi a kan tsanantar matsalar tsaro da kabilanci da Nijeriya ke fuskanta, ya na mai  cewa Buhari ne kawai ke da hurumin iya dakile matsalar.

A cikin wasikar, Obasanjo ya ce tashe-tashen hankula baya ga tsanantar rikicin kabilanci, ya hauhawa ne tun bayan hawan shugaba Buhari karagar mulki a shekara ta 2015.

Karanta Labaru Masu Alaka: Yadda Muka Hana A Tsige Obasanjo – Gowon

Obasanjo, ya ce rarrabuwar kawuna tsakanin kabilu da aka daina gani tsawon shekaru a Najeriya yanzu ta dawo sabuwa, inda kai tsaye ya zargi gwamnati  da jami’an tsaron akan rawar da su ke takawa.

A cewar wasikar, wadda ba ita ce karon farko da ya ke aike wa shugaba Buhari ya na sukar salon kamun ludayin sa ba, ya ce hanya daya ta magance matsalar da Nijeriya ta fada, dole ne Buhari ya jingine dabi’ar nuna kyama ko bambanci ko kuma kiyayya ga wasu kabilu.

A cewar Obasanjo, akwai bukatar ‘yan bindigar da ake alakantawa da makiyaya su fito su bayyana bukatun su, su zauna da gwamnati da nufin magance matsalar maimakon fadada ayyukan su na ta’addanci a sassan kasar nan.

Exit mobile version