Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kada A Sake Bari Masu Satar Kuɗin Talakawa Su Ci Bilis – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce duk wata shari’ar rashawar da aka samu matsala a kan ta saboda wasu uzurori alama ce ta tambaya, dangane da jajircewar ma’aikatan shari’a wajen yaki da rashawa.

Ya ce kada a daga wa duk wanda aka kama da rashawa ko zagon-kasa ga tattalin arzikin kasa, da kuma duk wani laifi na kudi kafa daga fuskantar hukunci.

Buhari ya ya sanar da haka ne, a wajen bikin bu]e wani taro na tsawon kwanaki uku da za a yi a Abuja, musamman domin wayar da kan ma’aikatan shari’a da masu bincike a kan rashawa da kuma mahukunta.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilci Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, ya ce ma’aikatan
shari’a su yi kokarin cike duk wasu guraben shari’a da masu laifuffukan cikin jama’a su ke boyewa a cikin su.

Ya kuma kara da jan kunne, inda ya ce kada shari’a ta tsaya a matsayin ‘yar kallo yayin da masu laifi ke amfani da damar sun a tsira da dukiyoyin al’umma.

Exit mobile version