Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Buhari Ya Dakatar Da Umarnin Biyan ‘Yan Gidoga Dala Miliyan 418 Daga Aljihun Jihohi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya dakatar da shirin da Ministar kudi Zainab Ahmed da Ministan Shari’a Abubakar Malami su ka kitsa don ya amince a fara ɗibar kuɗaɗen jihohi ana biyan wasu ‘yan kwangila, alhalin rikicin biyan kuɗin ya na kotu ba a kai ga yanke hukunci ba.

Wata majiya ta ce, a wajen taron Majalisar Zartaswa ta kasa na ranar 3 Ga Agusta ne, shugaba Buhari ya bada umarnin kada a fara cirar kuɗin bayan ya riga ya sa hannun amincewa a baya.

A baya dai rahotanni sun Ambato yadda Gwamnonin Nijeriya su ka rubuta wa Shugaba Buhari wasiƙar rashin amincewar su a kan fara cirar kuɗaɗen.

Yanzu haka dai ana cikin tafka shari’a a kotu, kuma kotun Ƙoli ta bada umarnin kada a fara cirar kuɗaɗen sai an kammala shari’a tsakanin masu dillancin kwangilar da ake rigima da su tukunna.

Yayin da Ministoci su ka hallara a wajen taron Majalisar Zartarwa ta kasa, sai Ministar kudi da Abubakar Malami su ka bijiro da batun cewa Shugaba Buhari ya gaggauta amincewa a fara biyan kuɗaɗen kawai.

Exit mobile version