Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Hukuncin Onnoghen: Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Nasara Ce Ga Kudirin Gwamnatin Buhari

Fadar shugaban kasa ta ce hukuncin da kotun kula da da’ar ma’aikata CCT ta yanke a kan tsohon shugaban alkalan Nijeriya Walter Onnoghen babbar nasarace ga kudirin gwamnatin shugaba Buhari.

Babban mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya ce sakamakon shari’ar Onnoghen ta nuna cewa, babu ruwan doka da girma kujerar ko matsayin mutum a gwamnati.

Garba Shehu ya ce amfanin doka ita duk wanda ya aikata ba daidai ba ta doka ta yi aiki a kan sa komin matsayin sa, sannan ya ce yaki da cin hanci da rashawa abu ne da ya shafi kowa, kuma ba an tsarashi ba ne domin musgunawa wani ko nuna banbancin siyasa ko wani abu ba.

Ya kara da cewa, ba za a samu nasara a kan yaki da cin hanci da rashawa ba, matukar masu fada a ji a gwamnati da sauran mukai suna samun kari’a shari’a, su kuma talakawa da masara karfi dokar na aikin a kan su ba.

Garba Shehu ya ce, wannan hukuncin zai zama darasi ga al’umma cewa, yaki da rashawa bai bar kowa ba, ko mutum ko dan Siyasa ne ko Alkali ko kuma ma’aikacin gwamnati ne to daka zata yi aiki a kan sa matukar ya taka ta.

Exit mobile version