Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dole Ne Jami’An Tsaron Najeriya Sa Ninka Ƙoƙarin Da Suke Yi – Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya zama wajibi
jami’an tsaron Nijeriya su ƙara himma matuƙar ana son a ciyar
da ƙasar nan gaba.

Tinubu ya bayyana haka ne, yayin ganawar sa ta farko da shugabannin hukumomi da rundunonin tsaron Nijeriya a fadar sa da ke Abuja.

Jim kaɗan bayan kammala tattaunawar, mai ba shugaban ƙasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Monguno, ya ce shugaba Tinubu ya shaida masu cewa ba zai lamunci yanayin da Nijeriya za ta riƙa samun koma-baya ba.

Ya ce dole ne samu haɗin kai tsakanin dukkanin ɓangarorin tsaro domin ganin an kauda duk wata matsalar tsaron da ke addabar Nijeriya.

Exit mobile version