Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sabon Rahoto Ya Bayyana Matsayin Da Ake Sa Ran Tinubu Zai Ba Kwankwaso

Rahotanni na nuni da cewa, akwai yiwuwar ɗan takarar
shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso
ya zama sabon ministan tsaron Nijeriya.

Wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa, ya nuna mai yiwuwa Kwankwaso ya zama ministan tsaro a karkashin gwamnatin Tinubu.

Wata majiya ta ce, duk da cewa akwai waɗanda ke son Shugaba Tinubu ya sa sunan Ganduje a majalisar ministocin sa, amma hankalin Tinubu ya fi karkata ga Rabi’u Kwankwaso.

A dalilin hakan ne, ake sa ran Kwankwaso zai shiga jerin sunayen ministocin da ake sa ran Tinubu zai bayyana a wata mai zuwa.

Majiyar ta ce wasu sun tura sunan tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, amma Tinubu ya fi karkata ga Sanata Rabi’u Kwankwaso, kuma akwai yiwuwar ya zama ministan tsaro.

Exit mobile version