Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dawo Da Daraja: Kungiyar Fulani Sun Yi Taron Neman Bakin Zare

Kungiyoyin Fulani makiyaya sun yi gagarumin taron neman bakin zaren dawo da martabar su a idon duniya daga kashin kajin da wasu ke shafawa mu su.

Kungiyoyin sun gudanar da taron ne karkashin kungiyar MIYETTI ALLAH a nan Abuja inda dukkan masu ruwa da tsaki su ka halarta.

Taron wanda ya nesanta dukkan Fulani daga ayyukan ta’addanci da nuna za a iya samun miyagu a kowace kabila, ya yi kira ga gwamnati ta rika hada kai da kungiyoyin Fulani wajen samar da maslaha.

Wakilin Lamidon Adamawa Dr.Abubakar Umar Girei ya ce in an ba fulani dama za a iya kawo karshen fitinar barayin daji a arewa ya ce kuma gwada su ko na mako daya ne a wata karamar hukuma za a ga sauyi.

Shi ma Shugaban kungiyar matasa makiyaya “JAM NDER FULBE” Kwamred Ahmad Muhammad Lamido ya ce su na daukar dukkan matakan cire baragurbi da masu shan kwaya daga matasan fulani.

A taron gamayar kungiyoyin makiyayan karkashin jagorancin, Baba Usman Ngelzarma, da tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ta karrama shaharerren malamin addinin musuluncin nan Malam Musa Yusuf Asadussunnah da sarautar Ardon Adalci kan yanda ya ke wayar da kai da fahimtar da al’umma halin da makiyayan ke ciki.

Ajawabin san a godiya Asadusunnah ya nanata kiran hada kai a arewa domin samun ci gaba mai dorewa.

Exit mobile version