Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsaro: Gwamnonin Arewa Sun Yi Wa Makiyaya ‘Yan Bindiga Afuwa

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina, ya ce gwamnonin Arewa sun yi wa barayin shanu da ‘yan bindiga afuwa, a wani tayin kokarin da ake yi na samun zaman lafiya a Arewacin Nijeriya.

Masari ya bayyana haka ne, a cikin wani jawabin bayan taro na kwana daya da gwamnonin Arewacin Nijeriya su ka gudanar a Katsina.

An dai yi taron ne tare da jami’an tsaro na bangarori daban-daban da ‘yan bijilante sa sauran kungiyoyin sa-kai, da makiyaya da kuma manoma.

Ya ce daga yau babu wani dan bijilante ko dan sa-kai da zai kara kai wa Fulani makiyaya hari ko kashe su haka kawai, kuma wannan sadaukarwa dukkan bangarorin biyu ne za su yi ta domin a samu dawwamammen zaman lafiya.

Masar ya bukaci a kyale makiyaya da iyalan su su rika zirga-zirgar su su na shiga kasuwanni da wuraren ibada, ba tare da cin zarafin su ba, matsawar dai ba dauke su ke da makamai ba, sannan maharan da su ka saci shanu a kauyuka su gaggauta maida su ga hannun hukuma ko kungiyar Miyetti Allah.

Exit mobile version