Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dattijan Igbo Sun Bukaci Kawo Karshen Hare-Hare Kan ‘Yan Kabilar A Lagos

Hadakar jagororin kabilar Igbo a karkashin gidauniyar kula da harkokin ‘yan kabilar wato ISCAF, ta bukaci Inyamuran da ke rayuwa a jihar Lagos su kauce wa maida martani dangane da hare-haren da ake kai masu a sassan jihar, lamarin da ke ci-gaba da tsananta tun bayan zaben shugaban kasa na watan Fabarairu.

Kungiyar, ta bukaci kasashen duniya su dauki matakin shiga tsakani tun kafin lamarin ya juye zuwa rikicin kabilanci.

Wata Sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce dole ne gwamnatin jihar Lagos da ta tarayya su biya ‘yan kabilar Igbo duk asarar da su ka yi sakamakon hare-haren da ake kai masu.

Kungiyar ta kara da cewa, ‘yan kabilar Igbo sun tafka asarar dukiya ta miliyoyi a hare-haren da ake kaiwa kan kadarorin su a jihar Lagos.

Yayin da ya ke jawabi a wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Owerri na jihar Imo, shugaban kungiyar Bishop Maglorious ya ce ‘yan kabilar Igbo su na fuskantar kyama a sassan jihar Lagos kawai saboda sun zabi son ran su.

Exit mobile version