Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Hare-Hare A Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kajuru, Mutum 2 Sun Rasu, An Yi Awon Gaba Da 5

Al’ummar Wasu Kauyuka A Zamfara Sun Koka Kan Hare-Haren ‘Yan Bindiga

Al’ummar Wasu Kauyuka A Zamfara Sun Koka Kan Hare-Haren ‘Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne a ranar Lahadi, sun kai hari yankin Adara da ke Buda a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna. Sun kashe Rabaren Alubara Audu da wasu mutum biyu tare da sace wasu mutum biyar.

Awemi Dio Maisamari, shugaban kungiyar kabilar Adara, a wata takarda ya jajanta aukuwar lamarin a yankin sannan ya yi kira ga hukumomi da su kawo karshen lamarin.

Kamar yadda Maisamari yace, “mugun harin da aka kai ya lashe rayukan mutum uku. Sun yi garkuwa da wasu mutum biyar a yankin. “Wurin daidai wannan lokacin, ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da mutum biyar daga yankin Kemara Rimi a gundumar Buda.”

A ranar Lahadi 16 ga watan Augustan 2020, an kai wani hari a kauyen Kalla da ke kusa da kogin Kaduna. Hakan ya janyo mutuwar wani mutum mai suna Danladi Abashi mai shekaru 50.

An samo gawarsa da taimakon ‘yan sanda saboda hana makiyaya shiga yankin Adara da aka yi

Exit mobile version