Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsage Gaskiya: Kungiyar Ohanaeze Ta Ce Babu Batun Biafra

Ohanaeze-Ndigbo

Shugaban ‘Yan kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo Farfesa George Obiozor yace babu yadda za’ayi su balle daga Najeriya domin kafa kasar Biafra kamar yadda wasu suke tunani, domin kuwa babu wata kabila dake cin gajiyar dorewar Najeriya zama kasa guda fiye da ‘yan kabilar Igbo.

Shugaban kungiyar ya ce babu wanda ya isa ya fitar da su daga Najeriyar duk da matsalolin da kasa ke fuskanta da kuma korafe korafen da kowanne sashe ke yi.

Farfesa George Obiozor ya bayyana cewar ‘yan kabilar Igbo a Najeriya kamar kifi ne a cikin teku, saboda haka mutu-ka-raba, domin babu wani tumbatsar ruwan da zai kora su zuwa tudu.

Yace ‘yan kabilar Igbo na zama a kowanne sashe na Najeriya inda suke gudanar da harkokin su na kasuwanci da sana’oi, abinda ya kaiga jama’a na fadin cewar duk inda kaga babu ‘dan kabilar Igbo toh ka gaggauta barin wurin.

Obiozor ya danganta matsalolin da ake samu a Najeriya da rashin shugabanci na gari da adalci wajen raba mukamai da dukiyar kasa da kuma rashin daidaito, inda ya bayyana fatar ganin ziyarar da shugaban kasa Buhari ya kai Jihar Imo zata bude kofar magance wadannan matsaloli.

Exit mobile version