Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Cire Tallafin Mai: Za A Fara Bai Wa Talakawa Dubu 8 Duk Wata

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci majalisar
dattawa ta amince da bukatar karbo bashin dala miliyan 800
domin amfani da su wajen rage wa talakawa radadin cire
tallafin man fetur.

Bukatar hakan dai ta na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban m,ajalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisar, inda shugaba Tinubu ya ce za a yi amfani da
kudin ne wajen habbaka shirin samar da zaman lafiya a Nijeriya, rancen da ya ce za a karbo shi ne daga Bankin Duniya.

Shugaba Tinubu ya kuma bada tabbacin cewa, gwamnatin tarayya za ta biya Naira dubu 8 duk wata ga marasa karfi miliyan 12 na tsawon watanni shida, kuma za a tura kudaden ne kai tsaye zuwa asusun wadanda za su amfana da su.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2023, shugaba Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur a jawabin sa na karbar mulki, lamarin da ya sa farashin man fetur yin tashin gwauron zabo.

Exit mobile version