Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Buhari Na Shirin Ciyo Bashin Dala Miliyan 800

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci Majalisar Dattawa ta amince ya ciyo bashin Dala miliyan 800.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci Majalisar
Dattawa ta amince ya ciyo bashin Dala miliyan 800.

Buhari ya gabatar da bukatar ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, wadda ya karanta a wani zama da ‘yan majalisar suka yi a ranar Talatar da ta gabata.

A cikin wasikar, shugaba Buhari ya ce za a yi amfani da bashin ne domin fadada wani shirin samar da walwalar jama’a musamman talakawa da gajiyayyu a fadin Nijeriya.

Shugaba Miuhammadu Buhari ya ce, za a ciyo sabon bashin ne daga Bankin Duniya.

Wannan dai ya na zuwa ne, a daidai lokacin da shugaba Buhari ke shirin mika mulki ga zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu .

Exit mobile version