Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ayyukan Jinkai Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Wa Talakawa Miliyam 20 Tallafi

download (23)

download (23)

Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin raba wa talakawan ƙasar guda 20 tallafin kuɗi domin rage musu raɗaɗin rayuwa.


Ministan kuɗi da tattalin arziki na ⁶ Wale Edun ne ya bayyana haka a lokacin babban taron tattalin arzikin ƙasar karo na 30 a Abuja, babban birnin ƙasar.


Mista Edun ya ce gwamnatin za ta yi amfani da ribar da ta samu a watanni shidan farko na shekarar 2024 wajen raba tallafin, domin inganta rayuwar talakawan ƙasar da ke fama da matsin rayuwa.


A jawabinsa na bikin zagayowar ranar ƴancin kai na 1 ga watan Okotoba, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin ƙasar ta samu ribar naira tiriliyan 9.1 a watanni shidan farkon shekarar da muke ciki.


Malam Abdulaziz Abdulaziz, ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban ƙasa Bola Tinubu ne, ya shaida majiyarmu cewa tallafin wata hanya ce da gwamnatin ƙasar ta ɓullo da shi domin rage wa talakawa raɗaɗin da suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur.

Exit mobile version