Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

CBN Ya Yi Ƙarin Kuɗin Ruwa Zuwa Kashi 18.5%

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya yi ƙarin kuɗin ruwa daga
kashi 18 zuwa kashi 18 da rabi cikin 100.

Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya sanar da haka, jim kadan bayan kammala taron kwamitin da ke kula ɓangaren a helkwatar Bankin da ke Abuja.

Wannan dai shi ne karo na uku da babban bankin Nijeriya ke ƙarin kuɗin ruwa.

Godwin Emefiele, ya ce ƙalubalen tsadar da ake fuskanta a fannin makashi na daga cikin dalilan da su ka haifar da ƙarin kudin ruwan.

Exit mobile version