Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Haraji: Bankin CBN Ya Zabga Harajin Ajiya Da Cirar Kudi A Bankuna

Babban bankin Nijeriya CBN, ya ce duk wani mai ajiyar kudi a banki zai fuskaci karin harajin ladar ajiya da cirar kudade a bankin da ya ke hulda da shi.

Daraktan Kula da Ajiyar Kudade na CBN Sam Okojere ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya aike wa dukkan bankunan da ke fadin Nijeriya.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya kai ajiyar naira dubu 500 zuwa sama, zai biya kashi 3 cikin 100 na kudin da ya kai ajiya, yayin da wanda zai cire naira dubu 500 zuwa sama zai biya kashi 2 cikin 100 na adadin yawan kudin da aka zuba.

Haka kuma, za a cire harajin kashi 5 cikin 100 idan asusun ajiyar na kamfanoni ko masana’antu ne daga adadin kudin da za a cire idan sun kai naira milyan 3 zuwa sama, idan kuma ajiya aka kai banki, za a cire ladar ajiya ta harajin kashi 3 cikin 100 na adadin kudaden idan sun kai naira milyan 3 zuwa sama. Babban bankin ya kara da cewa, karin da aka yi za a lafta shi ne a kan adadin kudaden da ake karba kafin wannan karin da aka yi, sai dai sanarwar ta ce, karin zai shafi wadanda ke hada-hadar kudade a bankunan da ke garuruwan Lagos da Ogun da Kano da Abia da Anambra da Rivers da kuma Abuja ne kadai.

Exit mobile version