Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi karin haske a kan wasu daga cikin dalilan da su ka sa ya dakatar da Godwin Emefiele daga jagorancin bankin CBN.
Tinubu ya yi karin hasken ne yayin tattaunawa da ‘yan Nijeriya mazauna Faransa a wata ziyarar aiki da ya kai, inda ya ce harkar hada-hadar kudi a karkashin Emefiele ta lalace a Nijeriya.
Ya ce wadanda ke zaune a wajen Nijeriya ba su iya tura wa iyayen su da ‘yan’uwan su kudi sakamakon farashin canji iri daban-daban.
Shugaba Tinubu ya cigaba da cewa, Nijeriya ta na da matsalolin tsaro, watakila ta haka su ke kara rura wutar rashin tsaro, don haka za a sauya tsarin hada-hadar kudi a Nijeriya.