Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tinubu Ya Gana Da Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele a fadar sa da ke Abuja.

Idan dai ba a manta ba, yayin da ya ke jawabi a wajen rantsar da shi, Tinubu ya bukaci bankin CBN ya yi dukkan mai yuwuwa wajen daidaita darajar kudin Nijeriya.

Shugaba Tinubu ya kuma sha alwashin yin garambawul ga sabon tsarin amfani da sabbin kudi da gwamnatin baya ta samar.

Ya ce akwai bukatar a rage kudin ruwa ta yadda za a janyo hankulan masu zuba jari, sannan za a daidaita tsarin kayyade farashin kayayyaki domin habbaka tattalin arzikin Nijeriya..

Bula Tinubu dai shi ne shugaba na uku da Godwin Emefiele zai yi aiki da shi, tun bayan da aka nada shi a matsayin gwamnan CBN.

Exit mobile version