Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Sanda Sun Rufe Majalisar Jihar Nasarawa Saboda Rikicin Shugabanci

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa, ta rufe Majalisar
Dokoki ta jihar domin gudun rikici, bayan an samu ɓangarori
biyu na ‘yan majalisar da ke adawa da juna.

A ranar Talatar da ta gabata, ɓangare ɗaya ya zaɓi Daniel Ogazi a matsayin kakakin Majalisar, yayin da ɗaya bangaren su ka zaɓi Ibrahim Balarabe.

Kakakin ‘yan sanda na jihar DSP Ramhan Nansel, ya ce Kwamashinan ‘Yan Sanda na jihar Maiyaki Baba ne ya bada umarnin rufe Majalisar bayan tattaunawa da sauran masana tsaro.

DSP Ramhan Nansel, ya ce ba za a bar kowane ɓangare ya shiga Majalisar ba har sai ƙura ta lafa.

Exit mobile version