Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Majalisar Tarayya Na Son a Yi Bincike Kan Dala Biliyan 25 Ta Gyaran Matatun Mai

Majalisar dokoki ta tarayya, ta nemi da a gudanar da binciken
ƙwaƙƙwaf bayan wani rahoton ta ya gano cewa an kashe sama
da dala biliyan 25 cikin shekaru goma wajen gyaran matatun
man Nijeriya.

Rahoton dai ya gano cewa, duk da wadannan ɗimbin kuɗin daaka kashe matatun hudu su na aiki ne ƙasa da kashi 30 cikindari.

Lamarin dai ya taso ne, yayin da farashin mai ya ninka bayan shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man da ya ce kasafin kuɗin da ya gada bai tanade shi ba.

Saboda rashin aikin matatun man yadda ya kamata tsawon shekaru, Nijeriya ta na fitar da ɗanyen man ta ne ta kuma sayo wanda aka tace daga kasashen waje.

Exit mobile version