Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Jonathan Ya Sanar Da Dalilin Dakatar Da Sanusi Lamido Sanusi

goodluck jonathan

goodluck jonathan

Tsohon Shugaban kasar, ya bayyana cewa dakatar da tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya faru ne saboda wasu laifukan kuɗi ba don batun zargin batan kuɗi da yayi ba.

Jonathan ya bayyana hakan ne a nan Abuja yayin ƙaddamar da wani littafi da tsohon Ministan Kudi, Dr. Shamsudeen Usman,

ya rubuta mai suna “Public Policy and Agent Interests: Perspectives from the Emerging World”a turance.

Jonathan ya musanta ikirarin Muhammadu Sanusi na cewa an dakatar da shi ne saboda ya fallasa zargin batan  dala biliyan 49.8 daga asusun gwamnatin tarayya.

Ya yi bayanin cewa an dakatar da Sanusi ne bayan tambayar da kwamitin rahoton kudi na Nijeriya (FRC) ya yi kan wasu kashe-kuɗaɗen da ba su dace ba a CBN.

Tsohon shugaban kasan ya kuma musanta zargin cewa Najeriya ta rasa wannan adadin kuɗin a lokacin mulkinsa, yana mai cewa kasafin kuɗin ƙasa a wancan lokacin bai wuce ya kai dala biliyan 31.6 ba kawai,

don haka ba zai yiwu a ce dala biliyan 49.8 sun bace ba tare da an lura ba.

Jonathan ya jaddada cewa bayan binciken kuɗi na PwC, an gano cewa dala biliyan 1.48 ne ba a bayyana ba, kuma an umurci kamfanin NNPC da ya biya wannan kuɗin cikin Asusun Tarayya,

ya kuma bayyana cewa binciken majalisar dattijai bai gano shaidar batan miliyoyin kuɗaɗen da ake zargi ba.

Exit mobile version