Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘yan bindiga sun kashe mutum 7, sun sace 26 a neja

‘Yan bindiga sun kashe mutane bakwai, tare da sace wasu 26
a karamar hukumar Mashegu ta Jihar Neja.

Shugaban karamar hukumar Umar Jibrin Igede ya tabbatar da harin da ‘yan bindiga su ka kai a wasu yankuna bakwai, inda ya ce hare-haren sun sa daruruwan mazauna yankin tserewa
daga gidajen su.

Umar Jibrin Igede ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun kashe daruruwan mazauna yankin tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekara ta 2023.

Ya ce a cikin makonni biyu da su ka gabata, ‘yan ta’adda sun kai hari a kauyukan Kulho da Sahon Rami, da Tashan Hajiya, kuma yawancin mazauna kauyukan da lamarin ya shafa sun bar gidajen su zuwa sansanin ‘yan gudun hijira da ke Kontagora da sauran wurare domin kare lafiyarsu.

A karshe ya yi kira ga gwamnatin jihar da sauran jami’an tsaro su kai masu dauki, domin kawo karshen hare-haren ta’addanci a karamar hukumar.

Exit mobile version