Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a kauyukan Galkogo da Zumba da ke cikin karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, lamarin da ya ba su damar kashe wani jami’in dan sanda, tare da harbin wasu yan sanda 3.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ASP Waslu Abiodun ya bayyana haka, inda ya ce ‘yan bindigan sun kai farmakin ne a kan babura fiye da 50, sannan sun kwashe fiye da sa’o’i biyu sun cin Karen su babu babbaka.
Mazauna kauyukan sun ce, bayan jami’an tsaron da ‘yan bindigan suka kai wa hari, sun kuma harbi wata karamar yarinya a ciki, da kuma wani mutumi da suka harba a cinya, kana kuma sun yi awon gaba da mutane da dama.
Dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Sanata Sani Musa ya aika wa manema labarai wasu bidiyon harin da ‘yan bindigan suka kai, inda ya bayyana damuwar sa game da halin rashin tsaro da al’ummar sa ke ciki.
Sanata Sani Musa ya bayyana cewa, al’ummar kananan hukumomin Shiroro fa Munya da, Rafi da Paikoro na fuskantar matsalar ta tsaro, sakamakon yadda ‘ yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke addabar su.
A karshe mai magana da yawun
rundunar ‘yan sandan jihar ya ce, tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamu
Usman ya tura da jami’an ‘yan sanda zuwa yankin domin tabbatar da tsaro.